Taiwan

Jami'an Tsaron Taiwan sun kama mutane kusan mutane 600

Yan sandan kasar Taiwan sun kama mutane 598, da suka hada da ‘yan kasar 410 da ‘yan China 181, bisa zargin gudanar da damfara ta kasa da kasa.An kama mutanen cikin Taiwan, China, Cambodia, Indonesia, Malaysia da Thailand, wadanda ke amfani da wayar tarho da hanyar Internet, wajen aikata laifuka.Babban jami’in ‘yan sandan Taiwan Wang Cho-chiun ya bayyana cewa wannan gagarumar nasara ce wajen kawar da miyagun aiyuka, kuma haka ya kassara aikin ‘yan damfaran.Yan sandan sun bayyana cewa za a fita keyar wadanda aka kama a wajne kasar zuwa Taiwan, kuma tuni aka kwace kudaden da sukakai dala milyan 1.33 daga wajen ‘yan damfaran.