Afghanistan-Pakistan

Shugaban Afghanistan Karzai zai kai ziyara Pakistan

Shugabana Afghanistan Hamid Karzai
Shugabana Afghanistan Hamid Karzai Reuters

Yau dinnan ne Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ke ziyara kasar Pakistan in da ake ganin alokacin wannan ziyara zai tattauna da ‘yan kungiyar Taliban domin neman zaman lafiya.Ziyayar tana zuwa makonni shida da kashe madugun Al-Qaeda Osama Bin Laden da Sojan Amurka suka yi a yankin Abbottabad na kasar Pakistan.Yayin ziyarar ta kwanaki biyu, Shugaba Hamid Karzai zai tattauna da Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari da PM Yusuf Raza Gilani.