Duniya

Taro kan canjin yanayi a Jamus

Canjin yanayi kamar yadda tassiwira ta nuna
Canjin yanayi kamar yadda tassiwira ta nuna CSI/ A. Robin

A yanzu haka wakilan kasashe guda190 ne ke halartar taro kan yadda za’a magance matsalar sauyin yanayi a duniya, wanda ake gudanarwa a Jamus.Sai taron na fuskantar kalubale inda ake cigaba da samun banbanci ra’ayi tsakanin kasashen da suka ci gaba, da kuma masu tasowa.Eve De Boer, na daya daga cikin masu bada shawara a taron.Ga kuma abun da ya ke cewa:“Ana samun tarnaki dangane da tattaunawar da ake, kasashe masu tasowa na bukatar a ci gaba da yarjejeniyar, amma Rasha, Japan da Cana na kin amincewa da haka, abin da ke kawo koma baya a taron.”