Yan Gudun Hijirar Kasar Suriya Na Karuwa A Turkiya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ana ci gaba da tashin hankali a kasar Suriya tsakanin masu zanga-zanga da dakarun Gwamnatin kasar. Mamayar da dakarun kasar ta Suriya suka yi wa yankin kan iyakar kasar da kasar Turkiya, ya sake haifar da wani sabon turmutsitsin yan gudun hijira, zuwa cikin kasar Turkiya mai makwabtaka da ita, wanda hakan ya sa Turkiyar kara kaimin aikin da take yi na gina wani katafaren kauye mai kunshe da tantunan saukar da yan gudun hijirarar.A garin Apaydin dake kudancin yankin Hatay Kilo mita 10 dab da kan iyakokin kasashen 2 sama da ma’aikata 150 a cikin tsananin zafin rana su ke ta ko karin kakkafa tantunan yan gudun hijirar, inda tuni kungiyar bayar da agajin jinkai ta Croissant Rouge a kasar Turkiya ta kafa tantuna 200.Mahukumtan Turkiya sun bayyana cewa, nan da mako guda za su samar da dubban tantuna a wani makeken fili mai fadin Eka 300.a yankin kan iyakar kasar da Syriya.