Somaliya

Ana ci gaba da kai agaji wa Somaliyawan da fari ya shafa

www.unocha.org

A karon farko, MDD ta kai kayan agaji cikin yankin Somaliya dake hanun kungiyar al-Shabaab wadda ake dangantawa da al-Qaeda.Wannan daidai lokacin da babban jami’an asusun kula da yara na majalisar, Anthony Lake, ya bayyana cewa farin da kasar ta Somaliya take fuskanta zai kara munana.Ya fadi haka yayin ziyara zuwa sansanin ‘yan gudun hijira Somaliya dake kasar Kenya.Lake ya ce lamarin na yunwa sakamakon fari zai shafi miliyoyin mutane cikin kasashen Gabashin Nahiyar Afrika, na wasu yankunan Kenya, Habasha da Djibouti.