Turai

Kasashen Turai za su sasanta Isra'la da Palasdinu

Reuters/Amir Cohen

KUNGIYAR Kasashen Turai na wani sabon yunkuri na ganin Isra’ila da Palesdinu sun cimma yarjejeya, kafin taron Majalisar Dinkin Duniya da ake ganin zai amince da kasar Palasdinu.Rahotanni sun ce, an samu rarrabuwar kawuna ataron da akayi makon jiya, tsakanin kasar Amurka, a bangare guda, da kuma kasashen Faransa, Russia da Kungiyar ta kasashen Turai, kan amincewa da birnin kudus a matsayin cibiyar kasar Yahudawa.Ko a cikin kungiyar ta kasashen Turai, Jamus da Italy na adawa da amincewa da kasar ta Palasdinu, yayin da Faransa da Spain suka bayyana karara cewar zasu goyi bayan aiyana kasar.