China

Ana zargin maharan China da samun horo a Pakistan

Reuters / Xinjiang Public Security Bureau

Kasar China ta zargi wasu mutane da ta ce an horar da su a Pakistan, da harin da ya hallaka mutane 14 a Kashgar.Hukumomin Yankin sun ce, binciken farko da suka gabatar ya nuna cewar, mutanen sun koyi hada bam ne a Pakistan.Ranar Lahadi data gabata, wasu mahara dauke da wukake ya hallaka akalla mutane cikin yankin Xinjiang na kasar China, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.Tashin hankalin ya faru hanyar Silk dake kaiwa garin Kashar, kuma jami’an tsaron sun tabbatar da faruwan lamuran biyu.Farkon wannan wata mutane 20 sun hallaka cikin garin Hotan, na wannan yanki dake kasar ta China, yayin artabu da jami’an ‘yan sanda.