Asiya

Farfadowar hanun jari cikin kasuwanni kasashen Asiya

Reuters

Kasuwanni a kasashen Asiya, sun farfado yau Litinin, sakamakon cimma yarjejeniyar da aka yi tsakanin Shugaban Amurka Barack Obama, da 'yan Majalisu, dan dage shinge bashin kasar.A Tokyo, Sydney da Seoul, farashin hannayen jari sun tashi da kusan kashi biyu, yayin da a Honk Kong farashin ya tashi da kusan kashi daya da rabi.