Siriya

An hallaka Masu zanga zanga 140 cikin kasar Siriya

REUTERS/YouTube via Reuters TV

Rahotanni Daga kasar Syria, sun ce akalla mutane 140 suka rasa rayukansu, sakamakon harin da soji suka kaiwa masu zanga zanga, a garin Hama.Wani jami’in kare Hakkin Bil Adama, Rami Abdulrahman, ya bayyana jiya Lahadi a matsayin daya daga cikin ranakun da aka fi zub da jini a kasar. Yayin da ake ci gaba da zanga zangar neman Shugaba Bashar al-Assad ya kaddamar da sauye sauyen demokaradiya.Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, da Kungiyar kasahsen Turai, sun yi Allah wadai da kisan.