Yemen

Mutane 15 sun hallaka a cikin rikicin kasar Yamen

رویترز

Hukumomin Kasar Yamen sun ce harin sama da aka kai a yankin Zinjibar da ke kudancin kasar, ya kashe akalla mutane 15 da ake zargin ‘yan kungiyar Al Qaeda ne.Cikin wadanda aka kashe har da wani mai suna Nader Shadadi, da ake ganin shine shugaban kungiyar a yankin. Jami’an tsaron kasar sun kuma ce an raunata mutane 17 cikin harin.Shugabannin sojan kasar Amurka da ke aiki a yankin sun yi ta nuna damuwa kan yadda 'yan al Qaeda ke amfani da rashi tartibiyar gwamnati, suna aiwatar da lamuran su.