Azumin-Ramadan

Yau Litinin kasashen Musulmai sun tashi da Azumi

Reuters/Vincent Kessler

Yau Litinin, al’ummar Musulmi a kasashe da dama ke fara azumin watan Ramadana, daya daga cikin shika shikan addinin Islama.A Nigeria, yayin da wasu suka fara azumin jiya Lahadi, mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bada umurnin fara azumin yau Litinin. Za a shafe wata guda ana gudanar da wannan Azumi, kamar yadda addinin Islama ya tanada.