Indiya

Hamshakin Mai Arzikin Indiya zai fuskanci bincike

Mukesh Ambani
Mukesh Ambani REUTERS/Arko Datta

Mutumin da ya fi kowa kudi a kasar Indiya, Mukesh Ambani na fuskantar yiwuwar bincike saboda wani katafaren gida mai hawa 27 da ya gina.Gwamnatin Jihar Maharashtra ta na tunanin tura masu bincike na kasar, don gano ko an yi almundahana wajen ginin, da yake daya daga cikin wadanda suka fi tsada a duniya.A shekarar da ta wuce Ambani, da shine na tara, a jerin masu kudi a duniya, ya shiga sabon gidan nashi.