Siriya

MDD tana tattauna rikicin kasar Siriya

REUTERS

Kwamitin Sulhun MDD ya shiga rana ta biyu bisa tattaunawa kan halin rikicin kasar, inda ake zanga zanga wa gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.Akalla mutane 24 sun hallaka cikin artabu da jami’an tsaro a garin Hama, ranar da Musulmai suka dauki Azumin watan Ramadan jiya Litinin. Haka ya janyo tir daga kasashen duniya.Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da demokaradiya sun facaccaki gwamnatin Siriya, kan yadda take daukan matakan da suka wuce kima wace murkushe masu zanga zanga.Tuni kasashen China da Rasha suka yi barazanar toshe duk wani kudirin MDD da zai kalubalanci gwamnatin kasar ta Siriya karkashin jagorancin Shugaba Assad.