Siriya

Dakarun Siriya sun mamaye garin Hama

REUTERS

Tankokin yakin kasar Siriya sun mamaye garin Hama na Tsakiyar kasar, domin kawo karshen zana zangar nuna kiyayya wa gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.Kugiyoyin kare hakkin bil Adama sun bayyana mutuwan mutane 90, tun ranar Lahadi da gwamnatin kasar ta kaddamar da farmaki kan mzasu zanga zanga. Wannan ya janyo tir da Allah wadai daga kasashen Yammacin Duniya.Wani mazaunin birnin na Hama, ya bayyana cewa an katse hanyoyin sadarwa, kuma gwamnatin kasar ta Siriya, ta neman amfani da shariyar tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak, wadda ke daukan hankali duniya, domin aikata abun da ta ga dama.