Japan

Majalisar Dokokin Japan ta amince da biyan diyya

REUTERS/Kyodo

Majalisar Dokokin kasar Japan ta amince da shirin kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa, ya biya biyya wa mutanen da lalacewar tashar nukiyar kasar ta shafa bayan faruwan Tsunami.Bisa tsarin za a samar da kudade na musamman wadanda za ayi amfani da su wajen biyan mutanen da rikicin tashar makashi Nukilya ta Fukushima ta shafa.Masu aiwatar da tashoshin nukiliya zasu hada gudumawa ta shekara , kuma za a biya kudaden da suka kai dala bilyan 100.