Siriya

MDD ta nuna damuwa kan halin da ake ciki a kasar Siriya

Rarrabuwar Kawuna a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya hana kwamitin daukar matsayi kan kasar Siriya, inda kasashen Rusha da China, suka ki amincewa da kalaman da aka yi anfani da su, a dabtarin da kasashen Turai suka gabatar.Tuni Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bayyana damuwarsa da halin da ake ciki a kasar ta Siriya, inda ya ke cewa, shugaba Bashar al Assad, ya rasa tunaninsa na Bil Adama.