Pakistan

Mutane 31 sun hallaka cikin rikicin garin Karachi na Pakistan

REUTERS/Athar Hussain

Akalla mutane 31 suka rasa rayukansu, a fadar kabilanci da ake ci gaba da yi a birnin Karachi, dake kasar Pakistan.Yan Sanda sun ce, an kashe mutane 11 jiya Talata, bayan 20 da aka kashe ranar Litinin, yayin da ake zargin magoya bayan Jam’iyun siyasar kasar, da hannu wajen tashin hankalin.