Syria

Assad ya yi Na’am da jam’iyyun adawa

Shugaban kasar Syria Bashar Assad.
Shugaban kasar Syria Bashar Assad.

Shugaban kasar Syria Bashir Assad ya gabatar da kudirin doka wanda ya shafi amincewarsa na samar da tsarin Jam’iyyu bayan tir da Allah waddai da Majalisar Dunkin Duniya ta yiwa gwamnatinsa na murkushe masu zanga-zanga ‘yan rajin tabbatar da demokradiyya a cikin kasar.Kafafen yada labaran kasar Syria sun ruwaito cewa shugaban ya gabatar da kudurin dokar ne na Jam’iyyu mai lamba 100 na 2011 a kundin tsarin zaben kasar.Tsarin samar da Jam’iyyu da dadewa na daya daga cikin muradun da masu adawa da gwamnatin Assad ke neman ganin an tabbatar tun bayan fara gudanar da zanga-zangar kin jininsa a watan Mayu.Sai dai kuma Wani rohoto da kungiyar kare hakkin biladama ta human right watch ta fitar ya nuna cewa mutane kimanin 2000 ne suka rasa rayukansu, daruruwansu kuma suka jikkata bayan da jami’an tsaron kasar suka bude wuta ga gungun masu zanga zanga.