Japan

Japan zata kori manyan jami’anta na cibiyar Nuclear

Wasu Mambobin kwamitin binciken matsalar makamashin Nuclear Fukushima
Wasu Mambobin kwamitin binciken matsalar makamashin Nuclear Fukushima 照片来源:路透社MANDATORY CREDIT REUTERS/Kyodo

Hukomomin kasar Japan sun sanar da dakatar da manyan ma’aikatan kula da cibiyar Nuclear kasar ta Fukushima sakamakon annobar da ta biyo baya a cibiyar makamashin Nuclear.A cewar Ministan cikin gidan kasar, ya zama dole su gudanar da sauye sauye domin sauya al’amurran cibiyar da ci gabanta. A cewarsa manyan jami’an cibiyar guda uku na sahun gaba cikin wadanda zasu irasa aikinsu.A 11 ga watan Mayu ne dai Kasar Japan ta yi fama da bala’in girgizan kasa da Tsunami da ta shafi cibiyar makamashin nuclear kasar.