Koriya ta Kudu

Babban jami'in MDD Ban Ki-moon zai kai ziyara kasar Japan

Babban jami'in MDD Ban Ki-moon, zashi kasar Japan gobe Asabar inda zai kasance wani kusa na farko daga waje da Hukumomin kasar zasu bari ya tafi yankin ma'aikatar Nukiliya dake Fukushima.Rangadin da zai kai har da yankin kabilarsa dake Koriya ta Kudu, domin jajantawa kasashen sakamakon hasarar rayukan jama'a da aka yi dan tsakanin nan.