Siriya

Dakarun sojan Siriya sun tsaurara matakai cikin garin Hama

REUTERS

Dakarun sojan kasar Siriya sun tsaurara matakan tsaro cikin garin Hama, inda ake ci gaba da bore nuna adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.Wannan ya nuna watsi da kirar da kasashen duniya ke ci gaba da yi na neman kawo karshen amfani da karfi kan masu zanga zanga, abun da ya janyo mutuwan mutane 2,000, kamar yadda alkaluman da Amurka ta fada ya nuna.Mazauna birnin na Hama sun bada rohoton mutuwan akalla mutane 135 daga ranar Lahadi zuwa yau Jumma’a.Garin na Hama nan ne mahaifin Shugaba bashar al-Assad, Marigayi Hafiz al-Assad ya tura da dakaru suka murshe boren da aka yi masa, abun da ya yi sanadiyar mutuwan dubban mutane.