Turai

Faduwar hanun jari cikin kasuwannin Duniya

REUTERS/Issei Kato

An sami faduwar darajar kasuwannin hannun jari a Asiya bayan hannun jarin Turai da Amurka, al'amarin dake haifar da fargaban afkawa cikin wata sabuwar matsalar tattalin arziki ta duniya.Bayanai na nuna cewa kasuwannin hannayen jarin sunyi ta faduwa daya bayan daya tun daga jiya alhamis har ya zuwa wayewar gari yau Jumma'a.Babban Bankin kasashen Turai, yayi tayin bada Karin tallafi, dan magance matsalar bashin da yake neman durkusar da wasu kasashen dake Yankin, ganin yadda tattalin arzikin Italy da Spain ke fadi tashi.