Siriya

Yan adawan kasar Siriya zasu yi taro a kasar Tunisiya

REUTERS/Social Media Website via Reuters TV (SYRIA

‘Yan adawa a kasar Siriya sun ce zasu gudanar da babban taron su a kasar Tunisiya bayan watan azumin Ramadan.Sanarwar ta zo sakamakon ci gaba da barin wuta da dakarun kasar ke yi kan masu zanga-zangan nuna kyamar Shugaban kasar Bashaer Al-Asad, wanda ya shiga kwana na shida a karin Hama.Kasar Amurka dai ta ce zata sanya kafar wando daya da mahukuntan kasar ta Siriya, kamar yadda Sakatariyar Waje na Amurkan, Uwargida Hillary Clinton ta bayyana.