Thailand

An Zabi Yingluck Shinawatra a matsayin Sabuwar PM Thailand

PM kasar Thailand Yingluck Shinawatra
PM kasar Thailand Yingluck Shinawatra REUTERS/Sukree Sukplang

Majalisar kasar Thailand ta amince da zaben Uwargida Yingluck Shinawatra a matsayin sabuwar PM kasar, wadda ita ce ta farko, mace da ta dare wannan kujera a kasar, ta kasance ita ce PM kasar ta 28.Yingluck Shinawatra ta kasance sabon shiga ce, cikin harkokin siyasa, domin bayanai na nuna cewa da bazar dan uwanta take rawa wato Thankshin Shinawatra tsohon PM, wanda aka kifar a juyin mulkin sojan kasar na shekara ta 2006.Bayanai na nuna cewa ta sami kuri'un wakilan majalisar kasar 296 daga cikin kusan wakilai 500.