Afghanistan-Amurka

Dakarun Amurka 31 sun mutu a Afganistan

Taswirar yankin  Wardak a Afganistan.
Taswirar yankin Wardak a Afganistan. RFI / Isabelle Artus

Dakarun yakin Amurka a Afganistan kimanin 31 ne suka mutu bayan harbo jirginsu mai saukar Angulu da kungiyar Taliban ta yi a yankin Wardak can kudu maso yammacin Birnin Kabul.Sanarwar dai ta fito ne daga fadar shugaban kasar Afganistan Hamid Karzai, tuni kuma shugaban ya mika sakon ta’aziyarsa ga shugaban Amurka Barrack Obama da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu.Tuni dai shugaban Amurka Barrack Obama ya jinjinawa dakarun Sojin da suka rasa rayukansu.