China

Fargaban Ambaliyar Teku A Kasar China

Fasalin ambaliyar tekun dake tafe a kasar China
Fasalin ambaliyar tekun dake tafe a kasar China rfi

Hukumomi a kasar China sun dauki matakai daban-daban domin kare bala'in mahaukaciyar ambaliyar ruwa dake tafe, daga teku, da ake kira Typoon Muifa.Bayanai na nuna an dakatar da zirga-zirgan jiragen sama a Shanghai, sannan kuma an kwashe mutane akalla dubu 500 dake zaune a gaban ruwan biranen dake kusa da teku gudun kada ayi hasarar rayuka.Masana sun hango igiyar ruwan tekun a sukwane, inda aka kiyasta gudun ya haura kilomita 178 cikin awa daya.