Ukrain

Alkalin kasar Ukrain ya yi watsi da bada belin tsohuwar PM Yulia Tymoshenko

Tsohuwar PM Ukrain Yulia Tymoshenko
Tsohuwar PM Ukrain Yulia Tymoshenko

Alkalin kasar Ukraine ya yi watsi da bada belin tsohuwar PM kasar Yulia Tymoshenko, kamar yadda lauyanta ya tabbatar.Ana tuhumar ‘yar siyasar da amfani da ofishinta ta hanyar da bata dace ba, kuma dubban magoya bayanta sun gudanar da zanga zanga a wajen kotun dake birnin Kiev.Yan sanda sun tsare tsohuwar PM Tymoshenko bisa rashin bada hadin ka iwa alkali, abunda aka dauka raina umurnin kotu, ta kuma kira alkalin da zama karan farautar Shugaba Viktor Yanukovich, babban abokin adawarta na siyasa.Tuni kasar Amurka da kasashen Turai suka yi tir da kamun da aka y iwa Tsohuwar PM kasar ta Ukraine Yulia Tymoshenko.