Tibet

An Rantsar da Sangay a matsayin Shugaban Tibet Masu gudun Hijira

Sabon Shugaban al'umar Tibet masu gudun hijira Lobsang Sangay da Dalai Lama
Sabon Shugaban al'umar Tibet masu gudun hijira Lobsang Sangay da Dalai Lama REUTERS/Adnan Abidi

An rantsar da sabon shugaban al’umar Tibet na kasar China masu gudun hijira Labsang Sangay.Sabon Shugaban Sangay ya yi karatu a Jami’ar Havard ta kasar Amurka, kuma a matsayinsa na shugaban Tibet masu gudun hijira, ya gaji mukamun Dalai Lama ke nan dan shekaru 76, wanda zai ci gaba da zama Shugaban addinin yankin.Lama yana cikin wadanda suka halarci bikin wanda ya gudana a kasar Indiya. Tun cikin watan Afrilu, Sangay dan shekaru 43 da haihuwa, ya lashe zaman zama PM, domin jagorantar al’umar Tibet dake fafutuwar neman kwar kwaryar ‘yanci daga kasar China.Sabon Shugaban ya yi alkawarin ganin ya kwato wa al’umar Tibet ‘yancinsu daga kasar China. Kuma wannan rantsuwa ta kawo karshen tsoron da ake ji, na cewa mutuwa ko tsuffar Dalai Lama, ka iya kawo karshen gwagwarmayar wadda aka fara tun shekarar 1959. Lokaci da su Lama suka tsere daga kasar China.