Siriya

Saudiya ta nemi Mahukuntan Siriya subi hanyoyin sulhu

REUTERS

Sarki Adallah bin Abdulaziz na Saudiya, ya janye jakadan sa daga kasar Siriya, saboda yadda hukumomin kasar ke ci gaba da murkushe 'yan adawa.A jawabin sa da aka yada a kasashen Larabawa, Sarkin ya bayyana tashin hankalin Siriya, a matsayin abinda ba za’a amince da shi ba.Rahotanni sun ce, a jiya Lahadi kawai an kashe masu zanga zanga sama da 80.