Yemen

Wani rohoto ya ce Amurka ta shawo kan Shugaban Yemen Saleh

Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh
Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh REUTERS

Jami’an kasar Amurka sun shawo kan Shugaban Yemen Ali Abdllah Saleh, domin kaucewa sake komawa kasarsa.Jaridun kasashen Larabawa sun ruwaito cewa an shawo kan shugaban, saboda kaucewa yuwuwar rikicin da komawarsa ka haifar. Amma jami’n jakadancin Amurka dake birnin Sanaa na Yemen, basu komai game da labarin.Jami’an kasar ta Yemen sun karyata labarin, kuma suka ce nan bada jimawa ba, Shugaba Saleh, dan shekaru 66 da hauhuwa, wanda ya shafe shekaru 33 kan madafun iko, zai koma gida.Shugaba Saleh ya shafe tsawon lokaci yana jinya a asibitin birnin Riyadh na kasar Saudiya, bayan harin da aka kai gidansa ya jikata shi.Tun wannan hari na watan Yuni aka samu kwarya kwaryar zaman lafiya cikin kasar ta Yemen.