France

Hannun Jari Na Amirka Na Farfadowa, Na Turai Na Tafiyar Hawainiya

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy. RFI

Kasuwan hannun jari na kasar Amirka ta sami farfadowa da safiyar yau Alhamis, yayinda Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ke kiran wani taro da Shugaban Gwamnatin Kasar Jamus Uwargida Angela Merkel domin tattauna batun basussukan kudaden Euro.Kasuwan hannun jari na Turai na ta tangal- tangal tun da safiyar yau Alhamis.Fargaba basukan kasar Girka da na Italiya ta sa Bankunan kasar Faransa cikin wani hali a yau.