Syria

Dakarun Syria sun bude wuta ga gungun masu zanga-zanga

Gungun Masu gudanar da Zanga-zanga a kasar Syria
Gungun Masu gudanar da Zanga-zanga a kasar Syria

Dakarun Syria sun bude wuta ga gungun masu gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bashar Al Assad a dai dai lokacin da ake shiga watanni 5 ana gudanar da zanga-zangar kin jininsa.Bayan kammala Sallar Juma’a ne dakarun kasar suka bude wuta ga gungun masu zanga-zangar a can gabacin birnin Deir el-Zour.An dai bayyana cewa mutane 2 sun rasa rayukansu bayan da dakarun suka bude masu wuta. Ranar Juma’a dai ta kasance ranar da aka ware domin gudanar da zanga-zanga a kasar Syria duk da murkushe masu zanga-zangar da gwamnatin ke yi.