Masar

An dage sauraren karar Mubarak zuwa watan Satumba

Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Moubarak, a gaban koto cikin keji .
Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Moubarak, a gaban koto cikin keji . Reuters/Egypt TV

An dage sauraren karar Hambararren Shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, zuwa 5 ga Watan Satumba wanda  ke fama da rashin lafiya da kuma ake tsare da shi cikin wani keji, bayan  sake gurfanar da shi gaban koto kan zargin cin hanci da rashawa, da kuma bada umurnin Murkushe masu zanga zanga.Mubarak dai zai gurfana gaban kotu ne tare da ‘yayansa guda biyu wadanda dukkaninsu ake wa zargin cin hanci da rashawa.Dubun dubatar ‘yan sanda ne aka girke dauke da makamai a harabar kotun da za’a saurari karar Hosni Mubarak domin kaucewa duk wata tanzoma dake iya aukuwa tsakanin masu kin jinin Mubarak da masoyansa.Idan dai kotun ta tabbatar da zargin da ake wa shugaban mai shekaru 83, to za’a yanke masa hukuncin kisa, bisa zargin bada umurnin kashe masu gudanar da zanga-zangar da ta kawo karshen mulkinsa a kasar Masar.Sama da mutane 850 ne dai aka kashe a kwanaki 18 da aka kwashe ana gudanar da zanga-zangar kin jin gwamnatin Hosni Mubarak.