Indiya

An cafke mai shirya zanga zanga a Indiya

'Yan sandan kasar Indiya
'Yan sandan kasar Indiya Online

Yan sandan kasar Indiya sun cafke daya daya daga cikin shugabannin kungiyoyin masu yaki da cin hanci, Anna Hazare, saboda shirya shiya yajin cin abinci, domin nuna adawa da wata doka.An cafke Hazare, wanda ya shirya shiga yajin abinci a Delhi babban birnin kasar, saboda dagewa da yayi na yajin dukda rashin amincewa da bada izinin haka daga jami’an ‘yan sanda.Ya dai nuna adawa ce da wata sabuwar ayar doka ta yaki da cin hanci da rashawa dake gabar majalisa, wadda ya kira abun dariya.