Syria

Palasdinawa 'yan gudun hijira suna tserewa daga Syria

Dubban ‘yan gudun hijiran Palasdinawa sun tsere daga sasanin dake garin Latakia na kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke murkushe masu zanga zangar kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce.Akwai ‘yan gudun hijira kimanin 10,000 da suka tsere, an kuma hallaka akalla mutane 30, cikin kwanaki uku da dakarun Siriya suka yi suna amfani da karfin tuwo kan masu neman Shugaba Bashar al-Assad ya yi murabus, a garin na Latakia mai tashar jiragen ruwa.Tuni kasashen Larabawa da sauran kasashen duniya suka yi Allah wadai da matakin da gwamnatin ta Siriya ke dauka, abunda ya kai ga tserewar ‘yan gudun hijiran Palesdinawan.