Siriya

Dakaru Syria suna ci gaba da far ma masu zanga zanga

Shugaban Syria Bashar al Assad
Shugaban Syria Bashar al Assad

Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da amfani da manyan makamai, domin murkushe masu yada kayar baya na garin Latakia mai tashar jiragen ruwa, kamar yadda mazauna birnin da masu raji kare hakkin bil Adama suka tabbatar.Akalla mutane 36 sun hallaka cikin boren na neman Shugaba Bashar al-Assad ya yi ban kwana da madafun iko, abunda ke ci gaba da yaduwa a biranen kasar.Kasashen duniya sun yi kakkausar suka kan matakan da gwamnatin kasar ta Siriya ke dauka na amfani da karfi kan masu zanga zanga.