Palasdinu

Palasdinawaza su mika bukatar samun kasarsu

Shugaban Paleasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Paleasdinawa Mahmoud Abbas Reuters/Mohamad Torokman

Shugaban kasar plastinu Mahmud Abas ya yi alkawalin ci gaba da bada hadin kai, ga kasar Amurka, a kokarin da palastinawa ke yi na samar da cikakkiyar kasarsu a MDD. A lokacin wani taron manema labarai a Sarajevo shugaba Mohmud Abbas, ya bayyana cewa babu shakka basa da niyar janye goyon bayansu ga Amurka haka itama Amruka bata da niyar janye goyon bayanta ga plastiinawa. A yinkurin Plastinawa na neman MDD ta amince masu da kafa cikakkiyar kasarsu kan iyakokinta na 1967.Shugaba Abbas ya sake nanata biyayar da suke yi ga kasashen Amurka da kungiyar tarayyar Turai, wadanda kuma yake fatan ci gaba da aiki da su domin su tallafa masu wajen ganin sun cimma burin da suka saka gaba na samar da yantaciyar kasasu.A lokacin babban zaman taron MDD na watan r gobe a birnin New York na kasar Amruka ne Plastinawa zasu gabatar da bukatar son amincewa da sabuwar cikakkiyar kasarsu.