Indiya

An sako mai rajin yaki da cin hanci na kasar Indiya

Yan sandan kasar Indiya sun sake mai raji yaki da cin hanci da rashawa na kasar Anna Hazare, wanda kama shi ya janyo zanga zanga a fadin kasa.Hazare ya ki barin harabar ofishin ‘yan sanda dake New Delhi babban birnin kasar, muddin ba a barshi yayi yajin cin abinci ba.Rahotanni sun bayyana sakin sauran magoya bayan Hazare fiye da 1000 wadanda suka cafke.