India

Ana Ta Zanga-Zangan Kyamar Cin Hanci A Kasar India

Magoya bayan Hazare na zanga-zanga
Magoya bayan Hazare na zanga-zanga RFI

Mai rajin yaki da cin hanci da rashawa na kasar Indiya Anna Hazare ya amince da sakin da ‘yan sandan kasar suka yi masa, inda zai yi yajin cin abinci na tsawon kwanaki 15.Wannan zai kawo karshen zanga zangar da magoya bayan Hazare keyi cikin biranen kasar ta Indiya, bayan kamun gwanin nasu dan shekaru 74 da haihuwa.Dubban magoya bayan sa sun yi zanga-zangan nuna goyon bayan su ga Hazare.Fira Ministan kasar Manmohan Singh ya fadawa najalisar kasar cewa abinda Hazare keyi kalubale ne gare su.