Japan

Cikin makon gobe jam'iyya mai mulkin Japan zata canja PM Naoto Kan

PM Japan Naoto Kan
PM Japan Naoto Kan AFP PHOTO/Toru YAMANAKA

Jam’iyyar DPJ (Democratic Party of Japan) mai mulkin kasar Japan, ta bayyana cewa cikin makon gobe zata zabi sabon shugaban, wanda zai maye gurbin PM Naoto Kan, a matsayin shugaban jam’iyyar da mukamun na PM.Sakataren jam’iyyar Katsuya Okada ya bayyana haka yau Litinin.Tun cikin makonnin da suka gabata ake saran PM Kan ya ajiye aiki, bisa sukar gwamnatin da ake yi, bayan girgizar kasa da igiyan ruwa na Tsunami da kasar ta fuskanta ranar 11 ga watan Maris, wadanda suka haifar da matsaloli wa tashashin nukiyar kasar masu samar da makamashi.Dubban mutane sun hallaka, tare da tagaiyara al’ummomin yankunan da aka samu bala’in.Duk wanda aka zaba, ana saran majalisar dokokin ta tabbatar da zabin zuwa ranar 30 ga wata na Agusta. Ministan Kudi Yashihiko Nada da Ministan Cinikayya Banri Kaieda ke kan gaba wajen iya lashe mukamun.