Asiya

Kasuwannin Hanun jari Asiya sun farfado

Reuters

Kasuwannin Hannayen Jarin Asia, sun farfado yau Litinin, yayin da farashin zinare ya yi tashi goran zabbi, inda ake saida shi akan Dala 1,878.Hannayen jarin Japan na Nikkei, ya samu maki 225, duk da zaman zulumin da ake saboda rikicin kasar Libya, yayin da farashin mai ya fadi da kusan Dala uku, inda aka yi odar man na watan Oktoba mai zuwa, akan Dala 106.