Kasashen Larabawa

Kungiyar Kasahen Larabawa ta yi suka kan harin Isra'ila a Zirin Gaza

REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Kungiyar Kasashen Larabawa ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kaddamar akan Yankin Gaza na Palesdinawa, wanda ya hallaka mutane 15, inda ta bukaci kasashen duniya da su tilasta mata kawo karshen sa.Kungiyar kasashen Larabawa ta yi kiran kawo karshen hare haren da Isra'ila ke kaiwa ne, a wata sanarwa da ta bayar, sakamakon harin da Isra’ila ta kaddamar, wanda yanzu haka ya lakume rayukan Palasdinawa 15, yayin da sama da 50 suka samu raunuka.Kungiyar ta kuma bukaci kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da ya dauki matakin da ya dace, na dakatar da hare haren.Har ila yau, kungiyar ta yi suka kan harin da Isra’ila ta kai kan dakarun kasar Masar, wanda ya kashe biyar daga cikin su.Ta kuma sake jaddada goyan bayan ta, kan shirin Palasdinawa na aiyana kasa ta kansu a zaman Majalisar Dinkin Duniya, na watan gobe.