Mongoliya

Mataimakin Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fara ziyarar kasar Mongoliya

Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden da 'yarsa Naomi
Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden da 'yarsa Naomi (REUTERS)

Mataimakin Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fara ziyarar kasar Mongoliya, inda ya yaba da yadda ake kara samun dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.Biden ya samu tarba daga Shugaban kasar ta Mongoliya Tsakhia Elbegdorj, a babban birnin kasar Ulan Bator.Wannan ziyara ce ta bakasafai ba, kuma anyi gudanar da bukukuwan al’adun gargajiyar kasar, mai makwabtaka da kasashen China da Rasha.