Majalisar Dinkin Duniya

MDD ta nemi bunkasa abinci da tsaftace ruwan sha

WikiMedia Commons

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, bunkasa hanyar samar da abinci da kuma tsabtacacen ruwan sha ya zama wajibi, saboda karuwar mabukata a duniya.David Molen, mataimakin Daraktan Hukumar dake kula da muhalli da kuma samar da ruwan sha, yace ganin matsalar da ake fama da shi a duniya, samo sabbin dabarun bunkasa samar da abinci da kuma ruwan sha, ya zama dole.