Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa ya fara ziyarar kasar Rasha

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong il
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong il

Shugaban Kasar Koriya ta Arewa dake ci gaba da ziyarar kasar Rasha, ya samu kyautar biredi da gishiri, kamar yadda ake girmama baki a Yankin Amur, yayin da matan garin suka ci ado, da jajayen kaya dan karbar shugaba Kim Jong Il da matarsa.Shugaban ya ziyarci wata tashar wutar lantarki, kuma ana saran yau Litinin, zai gana da shugaban kasar ta Rasha Dmitry Medvedev.