Siriya

Shugaban Siriya Assad ya ce gwamnatin kasar bata fuskantar rushewa

Shugaban Siriya Bashar al-Assad
Shugaban Siriya Bashar al-Assad AFP/Getty Images

Shugaban Kasar Siriya, Bashar al Assad, ya yi watsi da kiran da kasashen Yammacin duniya suka masa, na ya sauka daga mukaminsa, yayin da wakilan Hukumar Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya suka fara ziyarar kasar.Shugaba Assad ya ce kiran shugabannin ba shi da wani tasiri, domin ba a yiwa shugaban kasar da aka azaba irin wannna kiran, domin ba kasashen Yammacin Duniya suka nada shi ba. ya kuma kawar da yuwuwar rushewar gwamnatin kasar mai fusknatar bore daga masu neman girka demokaradiya.Yayin hira da tashar talabijin ta kasar Shugaba Assad ya ce lallai Siriya tana bukatar mafita ta siyasa amma ba tashin hankali ba. Masu raji kare hakkin bil Adama sun bayyana mutuwan akalla mutane 2,000 cikin watanni da aka kwashe dakarun gwamnatin kasar ta Siriya, na murkushe masu zanga zangar neman kawo sauye sauyen emokaradiya.