Siriya

MDD ta nemi bincike kan hallaka masu zanga zanga a kasar Siriya

. AFP PHOTO/STR

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta umurci gudanar da bincike kan yadda dakarun kasar Siriya ke cin zarafin Dan Adam, da kuma kashe mutane sama da 2,200.Hukumar ta ce, za’a gudanar da binciken ne daga watan Yulin da ya gabata zuwa yanzu. Gwamnatin kasra ta Siriya karkashin Shugaba Bashar al-Assad ta dauki matakan babu sani babu sabo kan masu zanga zangar dake neman gudanar da sauye sauyen demokaradiya.