Libya

Kasashen Afrika na Amince da 'yan tawayen Libya

Blaise Compaore Shugaban kasar Burkina -Faso da Muamamr Gaddafi
Blaise Compaore Shugaban kasar Burkina -Faso da Muamamr Gaddafi © AFP/Georges Gobet

Shugabanin Kasashen Burkina Faso da Chadi, sun yi tayin baiwa shugaba Mu'ammar Gaddafi mafakar siyasa, bayan amincewa da 'yan Tawayen kasar a matsayin shugabani.Kasashen biyu sun shiga cikin kasashe sama da 40 da suka amince da Yan Tawayen, inda suke cewa matakin na su, na da nasaba da zaman lafiya ne.Yau Shugaban kasar Fransa, Nicolas Sarkozy, dake ziyarar aiki kasar China, zai tattauna da shugaba Hu Jintao, kan halin da ake ciki a Libya, da kuma bashin kasashen Turai.Yayin da yake ganawa da wakilan Yan Tawayen Libya jiya, Sarkozy ya ce za’a ci gaba da fafatawa har sai magoya bayan Gaddafi sun aje makamai. Yau Alhamis PM kasar Italiya Silvio Berlusconi, ya gana dana 'yan tawayen Libya Mahmoud Jibril.