Faransa

Shugaban Faransa Sarkozy ya fara ziyarar kasar China

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Philippe Wojazer

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya isa birnin Beijing na kasar China, inda ya fara ziyara ta tataunawa da mahukuntan China kan matsalolin kudi da kasashen Turai suke ciki.Sarkozy zai shafe tsawon sa’o'i biyar yana ganawa da shugabannin kasar ta China, wadda take kasa ta biyu wajen karfi tattalin arziki tsakanin kasashen duniya bayan kasar Amurka.