Iran

Isra’ila ta san nayi a Gabas ta Tsakiya idan aka tattabatar da Palasdinu, inji Ahmadinajad

Shugaban kasan Iran Mahmud Ahmadinejad
Shugaban kasan Iran Mahmud Ahmadinejad FARS

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinajad yace kasar Isra’ila bata da wani hurumi a yankin gabas ta tsakiya idan har aka samar ta ‘yantartar kasar Palasdinu.Kalaman na shugaban na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar Iran ke gudanar da bukin ranar Kurdawa, ranar nuna goyon bayan tabbatar da Palasdinu tare da la’antar yahudawan Isra’ila.Da dadewa ne dai kasar Iran ke bayyana kyamarta ga Isra’ila tare da nuna goyon bayanta a fili ga kungiyoyi irinsu Hamas da Hezbollah ta Lebanon.A jawabin Ahmadinajad, shugaban ya yi kira ga kasashen Yammaci da su daina nuna goyon bayan Isra’ila, tare da bayyana kyamarsa ga yadda kasashen ke nuna goyon bayansu ga Isra’ila.Kasar Iran dai na fuskantar Matsin Labba daga kasashen yammaci bisa zarginta akan shirinta na makamashin Nuclear, al’amarin da kasar Iran ke musantawa.